<tr id="qc2ei"><optgroup id="qc2ei"></optgroup></tr>
<rt id="qc2ei"><xmp id="qc2ei">
<rt id="qc2ei"><xmp id="qc2ei">
<acronym id="qc2ei"></acronym><acronym id="qc2ei"><xmp id="qc2ei">
<acronym id="qc2ei"><xmp id="qc2ei">
Facebook Twitter
in Web www.davidkalish.com
Za a sake bude asibitin Xiaotangshan na Beijing
2020-01-29 17:29:53        cri
Daruruwan ma'aikata ne ke aiki ba dare ba rana, a jiya Talata, rana ta farko na fara aikin sake gina asibitin Xiaotangshan na birnin Beijing, da aka gina a shekarar 2003 domin kula da wadanda suka kamu da cutar SARS. Ana sake gina asibitin ne shekaru 17 bayan bullar waccan annoba.

A watan Afrilun 2003 ne aka gina asibitin Xiaotangshan a cikin kwanaki 7, da nufin dakile cutar SARS. Asibitin ya kunshi gadaje 1000, sannan ya kula da kimanin 1 bisa 7 na wadanda suka kamu da cutar SARS a fadin kasar, cikin watanni 2 bayan kammala shi.

An samu jayayya kan ko a bar asibitin bayan shawo kan cutar SARS, la'akari da cewa an gina shi ne cikin kwanaki 7 kuma ba a sanya galibin kayayyakin aikin asibitin yadda ya kamata ba.

A ranar 2 ga watan Afrilun 2010, shekaru 7 bayan shawo kan cutar SARS, hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta birnin Beijing, ta yanke shawarar rushe dukkanin dakunan marasa lafiya dake asibitin, inda a 2012, aka mayar da shi cibiyar yaki da cututtuka.

Duba da yawan wadanda suka kamu da cutar numfashi ta Coronavirus, ya zarce adadin wadanda suka kamu da cutar SARS ya zuwa 28 ga watan nan, sake gyara asibitin Xiaotangshan ya nuna jajircewar hukumomin Beijing na dakile annobar Coronavirus kafin ta ta'azzara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China

 

湖北11选5走势图